
Daga BELLO A. BABAJI
A ranar Laraba ne Majalisar Dattawa ta amince da sanya dokar ta-ɓaci da Shugaba Bola Tinubu ya yi a Jihar Ribas.
Saidai, a yayin zaman tattauna hakan ne Sanata Aminu Waziri Tambuwal da takwarorinsa – Sanata Seriake Dickson da Enyinnaya Abaribe suka fice cikin nuna rashin gamsuwa da matakin.
Haka kuma, a yayin zaman na sirri ne aka ga sanatoci ukun suna nuna kiyayyarsu ga sanya dokar da dakatar da wasu zaɓaɓɓun ƴan siyasa a jihar, inda suka bayyana hakan a matsayin saɓa wa dokar ƙasa.
Amma duk da boren nasu, majalisar sai da ta tabbatar da goyon bayanta ga hukuncin da Shugaban ƙasar ya yi da soke duk wata muhawara akan haka.
A yayin ganawa da manema labarai, Dickson ya yi godiya ga takwarorinsa da suke tafi akan ra’ayi ɗaya, ya na mai cewa Fadar shugaban ƙasa ta yi wasu gyare-gyare ga asalin abinda dokar ƙasa ta tanadar game da al’amarin.
Ya soki Shugaban majalisar, Godswill Akpabio kan ƙoƙarin rufe bakin ƴan adawa, ya na mai cewa kowane ɗaya daga cikin ƴaƴan majalisar yana da damar tofa albarkacin bakinsa, ba wai a mayar da wasu saniyar ware ba.
