Yadda Nijeriya ta yi fatali da tayin Dala miliyan biyar domin ta saki shugaban Binance

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Kamfanin Kirifto na Binance ya yi wa Nijeriya tauyin biyan Dala miliyan 5 a matsayin wani ɗangare na kuɗin haraji da ake binsa a ƙasashen nahiyar Afirka a ƙoƙarinsa na ganin an saki shugabanta a shekarar da ta gabata.

Kamfanin ya yi wannan tayi ne a watan Agustan 2024 bayan tsunduma tattaunawa domin sakin Tigran Gambaryan wanda ake zargi da aikata laifuka da suka shafi kuɗi.

An kama Gambaryan a ranar 26 ga watan Fabarairun 2024 saboda ƙin ba wa jami’an tsaro haɗin kai da ke binciken kan yadda kamfanonin kirifton ke gudanar da musayar kuɗi, ciki har da Binance a Nijeriya wacce ta zarge su da yi wa tattalin arziƙin Nijeriya zagon ƙasa da haifar mata da asara mai yawa. Sai dai an sake shi saboda dalilai na jinƙai a watan Oktobar shekarar bara duk da an cigaba da tuhumar da ake yi wa kamfanin.

Nijeriya ta ce Binance ya yi hada-hadar kuɗi ba bisa ƙa’ida ba. Ba tare da samun lasisin gudanar da ayyukansa ba da ƙin bin umarnin dokar yaƙi da safarar haramtattun kuɗi da ƙungiya-ƙumbiya wajen hada-hadar kuɗi.

Nijeriya ta kuma zargi Binance da samar da haramtacciyar kasuwar musayar kuɗi wanda ya bai wa masu sayar da Dala damar sai da ita a farashin da suke so wanda ya jawo taɗarɗarewar kasuwar canji.

Haka kuma, Nijeriya ta yi iƙirarin cewa Binance ta zame wa harkar canji barazana da zama silar hana masu zuɗa jari shigowa da kawo tangarɗa wajen biyan kuɗin shigo da kaya Nijeriya saboda tsarin gudanar da musayarsu da ba na gwamnati ba.

A cikin wata wasiƙa da ya aike wa da ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro mai ɗauke da kwanan watan 24 ga watan Fabarairu, kamfanin Kirifton ya amince cewa yana gudanar da ayyukansa a Nijeriya na tsawon shekaru 6 ba tare da rajista.

Kamfanin ya kuma yarda cewa a farkon shekarar 2024, tana da masu amfani da shafinsu a ƙalla 386,256 a Nijeriya tare da gudanar da hada-hadar kuɗi da ta kai Dala biliyan 21.6 da kuɗin shiga da ya kai Dala miliyan 35.4 a sheakrar 2023 kawai.

Bayan kama shugaban kamfanin, Gambaryan da Nadeem Anjarwalla (manajan nahiyar Afirka a kamfanin) a ranar 26 ga watan Fabarairun 2024. Nijeriya ta buƙaci Binance ya biya kuɗin harajinsa na tsawon shekara 4 (2020-2023) da biyan kuɗin ruwa na kaso 10 na kuɗin harajin da baya biya. Sai dai kamfanin ya gaza bin waɗannan kuɗi.

Daga nan, a wani zama da aka yi a farkon watan Agustan 2024, Binance ya yi iƙirarin samun kuɗin shiga na Dala miliyan 35.4 a 2023. ya ce ɗaukacin abin da ya samu a Nijeriya a shekaru 4 (2020-2023) ba zai wuce Dala miliyan 140. Kuma bayan buga lissafin, kuɗin da harajin da ake bin kamfanin zai kama Dala miliyan 7.

A wurin zaman tattaunawar ta hannun lauyanta, Arnold & Porter, kamfanin ya yi tayin biyan Dala miliyan 5. Sun ce za su saka kuɗin ne a wani asusun dillai masu shiga tsakani. Su ne za su biya kuɗin da zarar an saki Gambaryan kuma idan ya fice daga ƙasar nan.

Binance ta kuma amince da cigaba da tattaunawa da Nijeriya kan ba ta jerin sunayen mutane 100 da suka fi amfani da manhajar kamfanin da kuma alƙawarin ɗaukar kamfanoni biyu na Baker Tilly (akawu) da Chainalysis (masanin tafi da dandamalin intanet) domin gano ainihin nawa ya kamata kamfanin ya biya a matsayin haraji.

Sai dai Nijeriya ta kalli batun ba ta Dala miliyan 5 a matsayin wasan yara tare da neman lauyoyinta da su yi watsi da wannan tayi saboda rashin samun daidaito.

Sai dai Nijeriya ta fusata a lokacin da lauyoyin kamfanin suka sha alwashin bayyana cewa ana riƙe da Mista Gambaryan ne a matsayin fursuna kuma tabbas gwamnatin Amurka za ta ɗauki matakai a kan Nijeriya wanda hakan ya sa Nijeriya gaggauta janyewa daga tattaunawar.

“Idan ka kalli irin kasuwanci da asarar da aka jawo wa tattalin arziƙinmu, kamata ya yi mu nemi fin haka,” inji wata majiya. “Sannan tilas ne mu ƙarfafa buƙatarmu ta samun bayanai domin da su ne Nijeriya za ta iya buga lissafin girman kasuwanci da kuma harajin da muke bin Binance. A Amurka, kamfanin ya bayar da waɗannan bayanai ga hukumomi, mai zai sa yaƙi bai wa Nijeriya? Kamfanin Binance sun raina mu ne, suna ga ba mu kai ba su ba mu waɗannan bayanai.”

A yanzu Nijeriya na shari’a da Binance ne a kotuna biyu. ɗaya, a kan safarar haramtattun kuɗaɗe na Dala miliyan 35.4 wadda hukumar EFCC ta shigar da Gambaryan da Anjarwalla. Sai dai an jingine wannan ƙara a ranar 25 ga watan Nuwambar 2024 wata ɗaya kafin sakin shugaban Binance.

An zargi Binance karya sashe na 97 na kundin final kod kan haɗa kai da wasu wajen hada-hadar kuɗi da saɗa wa sashe na 58(5) na kundin dokokin banki da sauran laifuka da suka shafi kuɗi na shekarar 2020.

Sannan an zargi Binance da amfani shafinta wajen tattauna farashin musayar kuɗin waje a Nijeriya, ga shi kuma ita ba halastacciyar cibiya ba ce ta musayar kuɗi a Nijeriya. Wannan laifi ya saɗa wa sashe na 29(1) (c na kundin dokokin musayar kuɗin waje.

Sannan Binance ta saɗa wa sashe na 21 (a) wanda aka tanadi hukuncinsa a sashe na 18(3) na kundin dokokin safarar haramtattun kuɗi na shekarar 2022.

Nijeriya har’ila yau, a wata ƙara da hukumar tattara haraji ta shigar da Binance a ranar 19 ga watan Fabarairu, ta buƙaci kamfanin ya biya Dala biliyan 79.51 da Naira miliyan 231 a matsayin diyya saboda haifar wa Nijeriya asara sakamakon ayyukan kamfaninsa a Nijeriya wajen musayar kuɗin waje.

ƙarar da aka shigar a babbar kotu da ke Abuja ta buƙaci Binance ya biya Dala biliyan 2.001 a matsayin kuɗin harajin shekarun 2022 da 2023 inda ta zargi shugaban kamfanin Messrs Gambaryan da Anjarwalla da karya dokokin Nijeriya haɗi da ƙin rajista da hukumar FIRS domin biyan haraji da jawo wa Nijeriya asara.

FIRS ya yi zargin cewa Binance ya karya dokar kuɗin shiga da kamfanoni ke samu a Nijeriya kuma bincike ya nuna Binance ya fi shakaru 6 yana hada-hada a Nijeriya ba tare da rajista ba. Kuma shafin na da ‘yan Nijeriya 386,256 da ke amfani da shafukan kamfanin da yin kasuwanci da ya kai na Dala biliyan 21.6 da kuma samun riba da ta kai Dala miliyan 35.4 a shekarar 2023.

Jerin buƙatun FIRS:

–ƙin biyan haraji: Kan buƙatar cewa Binance ya kamata ta biya harajin a shekara saboda gudanar da kasuwanci mai muhummanci a Nijeriya.

–Kuɗin shiga: Akwai buƙatar Binance ta bayar da rahoton abin da ta samu daga 2022 da 2023.

–Biyan haraji: Neman Binance ta biya harajin Dala biliyan 2.001 na shekarar 2022 da 2023 tare da ladabtarwa da kuɗin ruwa.

–Biyan diyya kan asara ga tattalin arziƙin Nijeriya: Binance zai biya Nijeriya Dala biliyan 79.51 da Naira miliyan 231 na asarar da suka jawo wa Nijeriya.

–Ladabtarwa da ta haɗa da biyan kuɗin ruwa na kaso 10% a shekara kan kaso 26.75% na CBN har zuwa lokacin da za ta gama biyan harajin.

By ukarofi