Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya karrama gwarazan gasar karatun Alƙur’ani maigirma a fadar gwamnati da ke Kano.
A wata sanarwa da Kakakin gwamnan, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya aike wa Manhaja a ranar Talata, gwamnan ya jaddada aniyar gwamnatin sa wajen ci gaban karatun Alƙur’ani mai girma.
A yayin taron, gwamna Yusuf ya sanar da daukar nauyin karatun gwarazan su biyu, Gwani Sunusi Abubakar mai shekara 17 da Gwana Fatima Abubakar zuwa Jami’ar Al-Azahar da ke Egypt.
Baya ga haka, ya baiwa su biyun kujerun aikin Hajji da kyautar filaye da kuma kyautar kuɗaɗe.
Gwarazan ‘yan asalin jihar Kano ne, inda Gwani Sunusi Abubakar ya fito daga karamar hukumar Gezawa ya samu nasara a matakin kasa tare da Gwana Fatima Abubakar wadda ita ma ta samu nasara a matakin ƙasa.
Sauran waɗanda su ka zo na biyu da na uku su ma sun samu kyautar Naira miliyan 1 da kujerar aikin Hajji kowannensu.
