Kada ka yi gaggawar shiga wata maja – Tsohon shugaban ANP ga Kwankwaso

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Jigo a Jami’yyar NNPP kuma tsohon shugaban tsohuwar Jam’iyyar ANP, Asiwaju Moshood Shittu, ya shawarci jagoran NNPP, Rabi’u Musa Kwankwaso kan cewa kada ya amsa duk wata gayyata ko tayin shiga wata jam’iyyar haɗaka ta ƴan adawa.

Shittu ya bayyana hakan ne la’akari da abinda ya faru a shekarar 2014 na haɗa ƴan siyasa waje guda da nufin karɓe mulki a hannun tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Ebele Jonathan ba tare da zaɓo ƙwaƙƙwaran ɗan takara ba.

Ya ce, lallai akwai buƙatar Kwankwaso ya yi nazari game da wanda za a tsayar takara da manufar yin majar.

Ya kuma ce, ƴan siyasa suna rububin shiga jam’iyyar maja ba tare da samar da ɗan takara mai nagarta ba.

Tuni Kwankwaso ya zama jigo a harkar siyasar Nijeriya don haka ya ke da zaɓi kan yadda zai tafiyar da salonsa bisa kulawa da hangen nesa.

Shugaban yaƙin neman zaɓen Kwankwason ya ƙara da cewa, lallai gaggawar shiga waja maja ka iya haifar da da-na-sani matuƙar ba a samu ɗan takarar da zai iya ja da wanda ake son karɓe mulki a hannunsa ba.

By Babaji