Hukumar lafiya matakin farko ta inganta harkokinta a Nasarawa – Dakta Usman Saleh

Daga JOHN D WADA a Lafiya

Hukumar kiwon lafiya ta matakin farko ta gwamnatin Jihar Nasarawa ta ce a yanzu haka tana aiki tuƙuru ne tare da haɗin gwiwar babban bankin duniya da sauran abokan hulɗa wajen inganta harkokin ta na kiwon lafiya a faɗin jihar baki ɗaya.

Shugaban hukumar Dakta Usman Iskilu Saleh ne ya sanar da hakan a lokacin da yake karɓar baƙuncin ƙungiyar masu aiko da rahotanni, wato correspondents chapel a turance, ta ƙasa reshen Jihar Nasarawa a hukumar da ke Lafiya babban birnin jihar a makon da ake ciki.

Ya ce, a yanzu haka hukumar ta sabunta duka asibitocin jeka ka dawo sama da 50 dake jihar waɗanda a cewar sa hakan yana taimakawa wajen samar da ingantaccen kiwon lafiya ga jama’a tare da rage kuɗin da suke kashewa wajen neman lafiya da sauransu.

Dokta Usman Iskilu Saleh ya kuma bayyana cewa, ana sa ran kammala aikin kafin ƙarshen watan Yuni, sannan an shirya tabbatar da cewa dukkanin gundumomi 147 na jihar suna da asibiti ɗaya da ke aiki dare da rana.

Ya jinjina wa gwamnan jihar, Injiniya Abdullahi Sule, bisa jajircewarsa wajen bunƙasa fannin kiwon lafiya a jihar yana mai cewa gwamnan na ƙoƙarin tabbatar da cewa kowa yana samun ingantaccen kulawar lafiya a jihar baki ɗaya kawo yanzu tunda ya hau karagar mulki.

Bugu da ƙari, shugaban na hukumar kiwon lafiya na matakin farko a jihar ta Nasarawa Dakta Usman Iskilu Saleh ya buƙaci a samu haɗin gwiwa da hukumonin isar da labarai dabandaban a jihar da ma ƙasa baki ɗaya da sauran masu ruwa da tsaki domin wayar da kan jama’a kan muhimmancin kula da lafiya da zuwa asibiti don bincike da magani.

Tun farko, a jawabin shugaban ƙungiyar masu aiko da rahotanni ta ƙasa reshin Jihar Nasarawa Mista Isaak Ibgju yace ‘yan jaridar sun kasance a sakatariyar hukumar ne don taya sabon shugaban murnar naɗin sa tare da tabbatar masa cewa a shirye suke su cigaba da aiki tare da hukumar don samun cigaba musamman a fannin inganta harkokin kiwon lafiya a jihar baki ɗaya.