Ɗantata Salihu ya zama Sakataren Labarai na Gidauniyar Ilimin Matasa da Ci-gabansu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Gidauniyar Ilimin Matasa da Ci-gabansu, ta naɗa Mallam Ɗantata Salihu a matsayin Sakataren Yaɗa labaranta na Ƙasa.

Hakan ya biyo bayan kammala zama da masu-ruwa-da-tsaki na gidauniyar suka gudanar a Abuja ƙarƙashin jagorancin shugabanta, Hon. Kyari Jidai Gadzama, ranar Juma’a.

Za kuma a rantsar da shi tare da sauran mambobin majalisar zartarwar gidauniyar a ranar da aka tsayar.

Naɗin Salihu Ɗantata, wanda shi ne sakataren yaɗa labarai na farko a gidauniyar, an gabatar da shi ne na tsawon wa’adin shekaru biyar.

Manufofin Gidauniyar sune tallafa wa matasa masu burin yin karatu a ɓangarori daban-daban da samar masu da ayyukan yi gami da koya wa matasan da basu da aiki sana’o’in da za su dogara da kawunansu.

Ta kuma taya shi murna da fatan alkhairi wajen gudanar da harkokinsa bisa kula da kiyayewa.

By Babaji