
Daga BELLO A. BABAJI
Ɗan wasa Victor Osimhen ya zama ɗan wasa na biyu a tarihin Super Eagles wajen zura ƙwallaye mafi yawa, bayan da ya ci ƙwallaye biyu a wasan da Nijeriya ta yi da Rwanda na neman gurbin shiga gasar Kofin Duniya na shekarar 2026, ranar Juma’a.
Napoli ita ce ƙungiyar da ɗan wasan ya ke, duk da a yanzu yana matsayin na aro a Galatasaray, wanda ya zura ƙwallon farko ne a minti na 11, yayin da ya zura ta biyu ana dab da tafiya hutun rabin lokaci.
A yanzu Osimhen yana da ƙwallaye 25 a matsayinsa na ɗan Super Eagles, wanda hakan ya sa ya kere Segun Odegbami mai ƙwallaye 23.
Haka kuma, ƙwallaye 12 ne bambancin da ke tsakanin sa da Rashidi Yakini, wanda shi ne na ɗaya da ƙwallaye 37.
Ƙwallaye biyu da Osimhen ya zura sun yi sanadin yin nasarar farko ta koci tawagar, Éric Chelle.
Ga jaddawalin ƴan wasan da suka fi zura ƙwallaye a tarihin Super Eagles kamar yadda News Point Nigeria ta ruwaito:
“Rashidi Yekini (1984–1998) – 37 goals
Victor Osimhen (2017–present) – 25 goals
Segun Odegbami (1976–1982) – 23 goals
Yakubu Aiyegbeni (2000–2012) – 21 goals
Ikechukwu Uche (2007–2015) – 19 goals
Obafemi Martins (2004–2015) – 18 goals
Sunday Oyarekhua (1971–1976) – 17 goals
Samson Siasia (1984–1999) – 16 goals
Odion Ighalo (2015–2022) – 16 goals
Ahmed Musa (2010–present) – 16 goals.”
