
Daga BELLO A. BABAJI
Ƙungiyar Gwamnonin Nijeriya (NGF), ta cigaba da kare matakinta na yin shuru game da abubuwan da ke faruwa a harkokin siyasa a matsayinta na wadda ba ta da ɓangare a ire-iren batutuwan.
A wata takarda da ta fitar a ranar Asabar, NGF ta ce ɗaukar ɓangare a lamuran da suka shafi jam’iyyu ka iya sa kawunan mambobinta su rabu kasancewar su ƴaƴan mabanbanta jam’iyyu.
Hakan ya biyo bayan hukuncin sanya dokar ta-ɓaci a Ribas da Shugaba Bola Tinubu ya yi gami da dakatar da gwamnan jihar da wasu zaɓaɓɓun ƴan siyasa na tsawon watanni shida.
Takardar, wadda ke ɗauke da sanya hannun Darakta-Janar na ƙungiyar, Dakta Abdulateef Shittu, ta ce ƙungiyar ta fi mayar da hankali ne akan harkokin shugabanci da tsare-tsare a madadin rikice-rikicen siyasa da ke tsakanin jam’iyyu.
Bayanin ya biyo bayan kiraye-kiyare ne daga gidajen jaridu na neman NGF ta yi tsokaci game da ababen da ke faruwa a harkokin siyasa a yanzu.
Saidai, NGF ta ce manufofinta sune inganta tsare-tsare da haɗa kai da masu-ruwa-da-tsaki wajen ci-gaban tattalin arziƙi da walwalar al’umma.
Ya kuma tabbatar wa ƴan Nijeriya ƙungiyar za ta cigaba da mayar da hankali wajen shugabanci akan al’amuran da suka shafi ci-gaban tattali da walwalar al’umma.
