Kyaftin ɗin tawagar Faransa, Kylian Mbappe, ya ce zai yi farin ciki matuƙa gaya idan aka naɗa Zinedine Zidane, a matsayin mai horar da tawagar ƙasar.
A lokacin wata ganawa da aka yi da ɗan wasan, ya ce duk da cewa bai cika son yin magana kan wannan batu ba, kuma ba shi ke da haƙƙin naɗa mai horar da tawagar ƙasar ba, amma abu ne mai kyau idan har za a bai wa Zidane aikin horas da tawagar.
“Idan Zidane ya karvi horas da tawagar, zai zama abin farin ciki sosai, zan yi matuƙar farin ciki amma ba ni ne zan yanke hukuncin naɗa shi ba.
Idan dai ba a manta ba, mai horar da tawagar fa Faransa a yanzu Didier Deschamps, ya tabbatar da cewar zai aje aikinsa idan aka kammala gasar lashe kofin duniya ta shekara mai zuwa.
An daɗe dai ana alakanta tsohon mai horas da ƙungiyar Real Madrid Zidane, da aikin horas da tawagar ƙasarsa.
Mbappe dai ya kwana biyu bai haska ba a tawagar Faransa, sai a wannan karon da ya samu gayyata daga Deschamps, don buga wasan da za su yi da Croatia, a wasan daf da na kusa da na ƙarshe da za su yi a yau.
