DA ƊUMI-ƊUMI: Mahaifiyar gwamnan Jihar Katsina, Hajiya Safara’u, ta rasu

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Allah yayi wa Hajiya Safara’u mahaifiyar gwamnan Jihar Katsina Dikko Raɗɗa rasuwa bayan tayi fama da rashin lafiya.

Hajiya Safara’u Umar Raɗɗa ta rasu tana da shekara 93 da haihuwa.

Ɗaya daga cikin jikokin ta ya sanar da mutuwar,sai dai babu wani ƙarin bayani.

Yanzu haka dai gwamna Dikko Raɗɗa ya na ƙasar Saudiyya inda yake gudanar da Umrah.

By ukarofi