
Daga BELLO A. BABAJI
Tsohon Shugaban ƙasa, Goodluck Ebele Jonathan, ya ce dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara na Jihar Ribas da wasu zaɓaɓɓu zubar da martabar Nijeriya ne a idon duniya.
Jonathan, a yayin taron Gidauniyar ‘Haske Satumari Foundation Colloquium’ a Abuja, ya koka kan yadda aka cire zaɓaɓɓun jami’an daga jagorancin jihar, wanda hakan zai sa a riƙa yi wa ƙasar mummunar kallo.
Kalaman tsohon shugaban ƙasar sun biyo bayan sanya dokar ta-ɓaci ne da Shugaba Bola Tinubu ya yi a jihar, da dakatar da gwmanan da mataimakiyarsa gami da ƴaƴan Majalisar Dokokinta na tsawon watanni shida.
Shugaba Tinubu ya ce, ya yi hukuncin ne domin dawo da zaman lafiyar jihar da al’ummarta ganin yadda rikicin siyasa ya ƙi ce ya ƙi cinyewa a tsakanin Gwamna Fubara da ƴan majalisar dokokin.
Daga lokacin ne, Tinubu ya naɗa Vice Admiral Ibok-Ette Ekwe Ibas a matsayin jagora a jihar don ji da shugabancinta.
Saidai, Jonathan ya na ganin hukuncin a matsayin abinda zai haifar da koma-baya ga martabar Nijeriya, wadda tsarin zuba jari ya ta’allaƙa ne ga ayyukan zaɓaɓɓun jami’ai da harkokin shari’arta.
