Rufe VOA da Trump ya yi ya sanya Nijeriya da ƙasashen Afirka a tsaka-mai-wuya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Sanarwar dakatar da ayyukan gidan yaɗa labarai na VOA na Amurka da Shugaba Donald Trump ya yi, ya jefa Nijeriya da sauran ƙasashen Afrika shiga mawuyacin hali ganin yadda suka dogara da shi wajen samun labarai masu inganci da nuna ƙwarewa a yayin ayyukansa.

VOA, ɗaya ne daga cikin gidajen rediyon ƙasa-da-ƙasa da ke aiki bisa gaskiya da adalci ba tare da ɗaukar ɓangare ko nuna wariya ba, wanda hakan ya sanya al’ummar Afirka suka mayar da shi madogara wajen samun ingantattu kuma sahihan labarai.

A yayin da a wasu wuraren da gidajen jaridu ke samun kawunansu a ƙarƙashin kulawar gwamnati, akan ɗauki VOA a matsayin gidan da ke bayar da ingantacce kuma cikakken rahoto game da al’amuran da ke faruwa a yau da kullum.

Samuwar VOA ta bai wa al’ummomi karkara damar kunna rediyoyinsu don su sauraron labarai masu nagarta a ko’ina suke a duniya.

Harkokin demokraɗiyyar Nijeriya sun dogara ne da gidajen jaridu irin su VOA, wanda fage ne na tsage gaskiya da adalci a yayin da rufe shi zai haifar da sauya tunanin al’umma daga haƙiƙanin abinda ke faruwa a harkokin siyasa.

Haka kuma, ganin yadda kafar Soshiyal Mediya ta bai wa mutane da dama damar shigarta, wadda ke ɗauke da bayanai marasa asali, ya sa yaɗuwar labaran ƙarya da na ɗaukar ɓangare a harkokin siyasa suke tasiri acikin al’umma kasancewar babu nuna ƙwarewa a yayin yaɗa su.

Bugu da ƙari, rufe VOA ya jefa al’umma dama a Afirka cikin mawuyacin hali ganin yadda ƴan jarida da dama suka rasa ayyukansu, da ƙananan gidajen rediyo da suka dogara da VOA, waɗanda a yanzu sai dai su sabonta tsare-tsarensu.

By Babaji