
Daga BELLO A. BABAJI
A safiyar ranar Lahadi ne tsohon ɗan jarida a harkar ɗaukar hoto, Malam Zubairu Shaba ya rasu a Asibitij Koyarwa na Malam Aminu Kano dake Jihar Kano bayan fama da wani rashin lafiya.
Marigayin kafin rasuwarsa, ya yi aiki da gidajen jaridu na ƙasa, kana daga bisani ya shiga aiki da Triumph Publishing Company.
Ya kuma yi aiki da Hotline Magazine da Daily Trust da Market Magazine da sauran su.
Zubairu Shaba, wanda ya riƙe sarautar gargajiya ta Sarkin Ƙofar Patigi na Jihar Kwara, ya rayu ne da mata ɗaya da ƴaƴa 13 da kuma jikoki.
Za a cigaba da tuna shi bisa ƙoƙarinsa na shirya ɓangaren ɗaukar hoto a kamfanin Triumph, inda ya jagoranta har ya yi ritaya.
Al’umma na kai gaisuwar ta’aziyya a gidansa dake No21 Shagari Quarters, a Ƙaramar Hukumar Kumbotso, Jihar Kano.
