Hukumar Shari’ah ta Kano ta rabauta da bohol na sama da miliya N10 daga WAMY

Spread the love

Hukumar Shari’ah ta rabauta da Katafaren bohal na sama da Naira Miliyan 10 daga ƙungiyar World Assembly of Muslim Youth (WAMY) wanda aka ƙaddamar a harabar hukumar yau Alhamis.

Sheikh Ali Ɗan Abba da yake bayani a madadin shugaban hukumar yace dole ne su ƙara godewa Allah sannan mu godewa Ƙungiyar WAMY da suka gudanar da wannan gagarumin aiki na sadaƙatujjariya a wannan hukumar.

Ɗan Abba yace samar da rijiya mai sama da mita 150 abu ne mai daɗi, wanda duk wanda yazo wannan gida a baya razana yake amma wannan ƙungiya suka yi namijin ƙoƙarin wajen samar da ruwan akan kuɗi sama da Naira miliyan 10.

Shugaban hukumar Sheikh Abbas Abubakar Daneji ya yi fatan alheri ga wannan ƙungiya duba da irin yadda suka maida hankali wajen kyautatawa wannan hukumar ta shari’a “Wannan ba zai zama wani abin mamaki da wannan ƙungiyar ba, domin idan kuka kula kusan irin aiki ɗaya wannan ƙungiyar take yi da wannan hukumar” Ya kuma yi kira da sauran ƙungiyoyi da suyi koyi da ayyukan wannan ƙungiyar domin cigaban musulunci da musulmi.

Da yake nasa jawabin shugaban ƙungiyar WAMY Hisham Abdussalam yace duk lokacin da ya shigo wannan hukumar ko kuma ya ji sunanta wani farin ciki yake ji a zuciyarsa, don haka suka mai da kai wajen taimakawa wannan hukumar.

Ya kuma bayyana cewar ƙungiyar WAMY ta yi fice a ciki da wajen ƙasar nan domin ayyukan cigaban musulunci da musulmi ko ina suke.

Hukumar Shari’a da ke jihar Kano an kafa tane a shekarar 2003 ƙarƙashin jagorancin gwamnatin Malam Ibrahim Shekarau, kuma ita wannan hukuma tana gudanar da ayyukan tane akan duk abinda ya shafi addinin musulunci a jihar.

Hukumar ta sami dawamamme gata a wajen Gwamna Ibrahim Shekarau a wancan lokacin, sai dai bayan gushewarsa hukumar ta zama kamar kufai sabida lalacewa ba gyara.

Sai dai a yanzu Allah ya arzurta jihar da Gwamna Abba Kabir Yusuf me kishin jihar da hukumar, wanda yayi hangen nesa wajen zaƙulo mata ingantattun shuwagabannin da za su gudanar da ita masu kishin addini da aikin gidan. Don haka muke fatan Gwamna Abba zai fita Zakka wajen dawo da wannan hukumar hayyacinta kamar a farkon ta ko ma ta wuce haka kamar yadda Musa A Ibrahim ya sanya hannu a takardar sanarwar

By ukarofi