Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Bisola Kola-Daisi, ɗiya ta farko ga tsohon gwamnan jihar Oyo, marigayi Sanata Abiola Ajimobi ta rasu.
Marigayi Bisola ta rasu tana da shekaru 42 a duniya a birnin Landan na kasar Birtaniya.
Mai bai wa tsohon gwamnan shawara na musamman, Bolaji Tunji ya tabbatarwa manema labarai faruwar lamarin a Ibadan ranar Alhamis.
Har zuwa rasuwarta, ta kasance mai ba Ministan Kasafin Kuɗi da Tsare-tsare, Atiku Bagudu shawara na musamman.
