Ka guji ƙara aure idan ka na fama da talauci – Sarkin Zazzau

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Mai Martaba Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Nuhu Bamali, ya shawarci mazajen da ba su da ƙarfi da su manne wa mace ɗaya kawai, domin su tara iyalai.

Sarkin ya koka kan yadda auren mata fiye da ɗaya ke wargaza iyalai, saboda wasu mazajen sun gaza wajen gudanar da ayyukansu.

Da yake jawabi a wajen rufe taron shekara-shekara na ƙungiyar Mata Musulmi ta Nijeriya (FOMWAN) karo na 30, Sarkin ya ce saboda Musulunci ya bai wa maza ’yancin auren mace fiye da ɗaya, ba yana nufin kowane namiji zai iya ciyar da masu dogaro da shi ba.

“A cikin gida, sai ka ga akwai iyalai 192 da ke zaune a ciki kuma a cikinsu, za ku ga wani mutum mai ‘ya’ya sama da 50. Ta yaya zai iya kula da su?” ya ce.

Daga nan sai ya yi kira da a sake nazarin manhajoji a tsarin ilimin islamiyya, domin a haɗa da ‘yancin ‘yan mata a Musulunci.

Wannan, a cewarsa, zai canza tarihi kuma tare da gina al’ummomi masu inganci da nagarta.

Ya zargi alƙalai da haddasa matsalolin al’umma, inda ya buga misali da wata budurwa da aka yankewa hukuncin ɗaurin shekaru biyu a gidan yari saboda rashin biyan bashin N6,000.

“A ranar da na je gidan yarin, Naira 200,000 kawai nake da ita amma na samu nasarar sakin mutane takwas,” inji shi.

Ya yi nuni da cewa fadar na ci gaba da amfani da Alternative Dispute Resolution (ADR) wajen magance matsalolin aure, gado da rigingimun filaye, ya ƙara da cewa, “Waɗannan al’amura su ne illa ga iyalai da dama.

A nata jawabin, mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna, Dakta Hadiza Sabuwa Balarabe, ta buƙaci malamai da su ƙarfafa mazaje su rungumi aikin da Allah ya ɗora musu.

“Akwai buƙatar malaman mu su ƙarfafa maza su ɗauki nauyin da ya rataya a wuyansu a gida domin an gano cewa mafi yawan ayyuka a yanzu mata ne ke ɗaukar nauyinsu,” inji ta.

By ukarofi