Ɗiyar tsohon gwamna a Nijeriya ta rasu a ƙasar Birtaniya

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Bisola Kola-Daisi, ɗiya ta farko ga tsohon gwamnan jihar Oyo, marigayi Sanata Abiola Ajimobi ta rasu.

Marigayi Bisola ta rasu tana da shekaru 42 a duniya a birnin Landan na kasar Birtaniya.

Mai bai wa tsohon gwamnan shawara na musamman, Bolaji Tunji ya tabbatarwa manema labarai faruwar lamarin a Ibadan ranar Alhamis.

Har zuwa rasuwarta, ta kasance mai ba Ministan Kasafin Kuɗi da Tsare-tsare, Atiku Bagudu shawara na musamman.

By ukarofi