An kama ɗan fashin da ya kashe mai POS a Adamawa

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hukumar ‘yan sanda a jihar Adamawa ta ce ta kama wani mutum da ake zargi da hannu wajen kashe wani mai sana’ar PoS, Abbas Yuguda, a ƙaramar Hukumar Mayo-Belwa ta jihar ranar Asabar.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Yahaya Nguroje, ya bayyana a wata sanarwa a ranar Litinin cewa Yuguda, yayin da yake dawowa daga sana’arsa, wasu gungun ‘yan fashi ne suka kai masa hari tare da raunata shi, suka bar shi cikin tafkin jini.

Nguroje ya ƙara da cewa, da samun labarin faruwar lamarin, jami’an ‘yan sanda sun ziyarci wurin, inda suka samu Yuguda, suka garzaya da shi wani asibiti da ke kusa, inda ya mutu a lokacin da ya ke jinya.

Ya ƙara da cewa, “Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta ƙaddamar da bincike kan wani mummunan kisan da aka yi wa wani sana’ar POS, Abbas Yuguda, ɗan shekara 35, wanda aka kai wa hari a ƙaramar hukumar Mayo-Belwa.

“Al’amarin ya faru ne a ranar 22 ga Maris, 2025, a lokacin da wanda abin ya shafa ke kan hanyarsa ta komawa gida bayan rufe shago daga harabar kasuwancinsa, wasu gungun mutane ɗauke da muggan makamai suka kai masa hari tare da yi masa munanan raunuka inda suka bar shi kwance cikin jini.

“Jami’an ‘yan sanda da ke ofishin ‘yan sanda, Mayo Belwa, sun isa wurin, inda nan take suka garzaya da wanda abin ya shafa zuwa asibitin Cottage, Mayo-Belwa, a ƙoƙarin ceton ransa, amma abin takaici, an tabbatar da mutuwarsa a lokacin da ya ke jinya”.

Ya ci gaba da cewa, wasu matasa a yankin da lamarin ya faru sun bi sawu inda suka kama ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin ’yan fashi da makamin kuma suka damƙe shi.

Kakakin ya ƙara da cewa, ‘yan sanda sun shiga tsakani domin ceto wanda ake zargin daga hannun matasa, wanda aka kwantar da shi a asibiti.

Ya gargaɗi mazauna jihar kan ɗauakar doka a hannu tare da buƙatar su da su kai rahoton duk wani abu da ya faru ga ‘yan sanda.

By ukarofi