Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Wasu maharan da ake kyautata zaton ’yan Boko Haram ne sun kashe sojojin Nijeriya da dama, yayin da wasu da dama suka jikkata a jihar Borno.
Al’amarin ya faru ne a lokacin da ’yan bindigan suka kai hari kan sansanin soji da ke Wajirko a Damboa da sansanin soji na Wulgo a Gamboru Ngala da yammacin ranar Litinin.
Wasu rahotanni sun bayyana cewa a yayin harin kuma an kashe wasu daga cikin mayaƙan na Boko Haram.
Haka kuma wasu rahotanni na ce kwamandan sojin da ya kai ɗauki ya taka nakiya da ta fashe, lamarin da ya janyo karin jikkata wasu da ma rasa rayuka.
Sansanin na Wulgo na bakin iyakar jamhuriyyar Kamaru, kuma yana ɗauke da sojin haɗaka na Nijeriya da ƙasar ta Kamaru.
