
Daga BELLO A. BABAJI
Tsohon Mataimaki na Musamman kuma Daraktan Bincike da Tantancewa a Gwamnatin Malam Ibrahim Shekarau a Jihar Kano, Malam Ibrahim Ado Kurawa, ya yi watsi da batun soke hawan sallah da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya yi a yayin shirye-shiryen Sallah.
Ado Kurawa, wanda mawallafi ne kuma mai bincike, ya bayyana wa manema labarai a ranar Alhamis cewa, Aminu Ado ba shi da hurumin yin kira ga hawan sallah ganin yadda ya rasa damar hakan a gargajiyance.
Ya ce, ba zai yiwu a ce ya sauya tsarin hawan sallah da aka ɗauki shekaru sama da 500 ana gudanarwa a jihar Kano ba, ya na mai cewa sanarwar hawan da ya yi, abu ne da aka siyasantar da shi da nufin tada zaune-tsaye.
Haka kuma, Kurawa, wanda shi ya rubuta littafin da ke bayani game da hawan sallah, wanda UNESCO ta yaba da shi, ya ce Aminu Ado ba shi da wasu ƴan majalisar sarki kamar su Shamaki, Madakin Ɗan Rimi da Sallama, waɗanda suna da gagarumar rawa da suke takawa yayin gudanar da taron.
Sannan akwai Makaman Kano, wanda shi ke jagorantar shirye-shiryen da ake gudanarwa a yayin bikin, kuma ba ya tare da Aminu Ado.
Bugu da ƙari, ya ce a yayin da Sarki zai je hawan, sai ya sanya fararen kaya kuma ya taho ta wata ƙofa da ake kira da Ƙofar Fatalwa, inda daga nan ne zai tafi filin Idi a ƙafa.
A cewar Kurawa, tunda Sarki Aminu Ado ba daga gidan Rumfa ya ke gudanar da harkokinsa ba, ba shi da ikon jagorantar bikin.
