NUJ ta raba wa iyalan ‘yan jarida da suka rasu kuɗi da abinci a Kebbi

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

Kamar yadda ta saba kowace shekara, ƙungiyar ‘yan jarida ta jihar Kebbi bana ma ta rabawa iyalan ‘ya’yan ƙungiyar da suka rasu kayan abinci da kuma kuɗi.

 An gudanar da taron rabon kayan a harabar gidan talabijin mallakar jihar Kebbi ranar Litinin ɗin da ta gabata.

Da ya ke tofa albarkacin bakinsa, kwamishinan yaɗa labarai na jihar Honarabul Ahmed Yakubu Birnin Kebbi ya yaba wa ƙungiyar ‘yan jaridar bisa ga irin wannan tunanin na tuna abokan aikin su da suka kwanta dama.

Ya ce wannan tunanin ya yi daidai da irin tsare-tsaren mai girma gwamna Nasir Idris na raba tallafi ga al’ummar jihar musamman mabuƙata da ma’aikatan gwamanati.

Ya kuma bayar da tabbacin samun goyon bayan gwamnatin jihar Kebbi a duk lokacin da ƙungiyar ta zo da wani shiri nan gaba.

Hakazalika mai bai wa gwamna shawara kan kafafen yaɗa labarai Yahaya Sarki ya yaba wa ƙungiyar ‘yan jaridar bisa ga tabbatar da dugadugan ta bisa ga wannan aikin da ta daɗe tana aiwatarwa tsawon shekaru inda ya yi alƙawarin bayar da na sa gudummawa a duk lokacin da irin wannan aikin ya taso.

Daga ƙarshe shugaban ƙungiyar Alhaji Bello Sarki ya bayar da tabbacin cigaba da aiwatar da wannan shirin da tsohon shugaban ƙungiyar Alhaji Aliyu Jajirma ya ƙirƙiro na taimakawa iyalan ‘yan jarida da suka rasu.

Ya kuma yaba wa Alhaji Umar Idris Buro, Engineer Rilwanu Usman na Ganou Rice Farm, Labana Rice da kuma kwamishinan kananan hukumomi da masarautu na jihar Kebbi bisa ga rawar da suka taka don ganin an samu nasarar aiwatar da wannan shirin.

ƙungiyar dai ta raba aƙalla buhunan shinkafa ashirin da biyu da kuma kimanin naira miliyan ɗaya ga sassan ƙungiyar guda shida.

By ukarofi