Rufe tafsir: Babban limamin Jos ya nemi haɗin kan malamai da shugabanni

Spread the love

Daga HABU ƊAN SARKI, Jos

Babban limamin Jos, Sheikh Ghazali Isma’ila Adam ya rufe tafsirin sa na wannan shekara ta 2025 tare da kira da malaman addinin Musulunci da shugabanni su haɗa kansu a matsayinsu na masu faɗa a ji a cikin al’umma, don samar da haɗin kan mabiyansu da zaman lafiya.

Ya kuma buƙaci sauran al’ummar musulmi su cigaba da yin riƙo da kyawawan halayen da suka tarbiyyantu da su a cikin watan Ramadan, don samun ƙarin kusanci da Allah, da yin rayuwa ta ƙwarai da za ta kare kimar su da ta addinin Musulunci.

Babban limamin ya bayyana hakan ne a yayin rufe tafsirin sa na wannan shekara a babban masallacin Jumma’a na Jos, wanda ya samu halartar manyan malamai, ‘yan siyasa da masu faɗa a ji a cikin Jos.

Tafsirin na bana ya fara ne daga Surat al-Fatiha zuwa Surat Ali Imran, yayin da cikin tsawon makonnin da aka shafe ana gudanar da wannan tafsiri aka riƙa ƙarfafa gwiwar musulmi kan riƙo da koyarwar addinin Musulunci, biyayya ga shugabanni, da ƙarfafa zaman lafiya a tsakanin mabambantan mazauna garin Jos da Jihar Filato baki ɗaya.

Sauran waɗanda suka halarci taron rufe tafsirin da suka haɗa da shugaban al’ummar musulmi, Turakin Jos, Alhaji Garba Abdulƙadir da Makaman Jos ta Arewa, Alhaji Sani Mu’azu, tsohon shugaban Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa, Alhaji Sani Mudi sun ƙarfafa kira ga zaman lafiya a tsakanin musulmi da kirista, riƙo da koyarwar addinin Musulunci, da gudanar da bukukuwan sallah cikin lumana.

An gudanar da addu’o’i na musamman domin samun zaman lafiya da tsaro, da bunƙasar tattalin arziƙi a cikin Jihar Filato da Nijeriya baki ɗaya.

By ukarofi