Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano
Yanzu haka an zaɓi tare da rantsar da Hon. Bello Jadda Sharifai mai bawa Gwamanan Kano shawara a kasuwar waya ta titin Beruit Kano kuma sabon Shugaban ƙungiyar kasuwar waya ta kasuwar Beruit wanda aka zaɓa a matsayin shugaba kuma aka rantsar da shi da mataimakan sa a ofishin kwamishinan ciniki da masana’antu Alhaji Shehu Wada Sagagi bayan an gabatar da zaɓen a ranar Asabar da ta gabata.
Haka kuma sabon shugaban ƙungiyar ya yi alwashin warware matsalolin kasuwar kamar hasken wutar lantarki inganta tsaro da kyakyawar mu’amala tsakanin ‘yan kasuwar da kuma masu zuwa kasuwar don saye da sayar wa da sauransu ya kuma nemi haɗin kai ga ɗaukacin masu ruwa da tsaki a wannan kasuwa da ma Jihar Kano bakiɗaya.
A ƙarshe ya yaba wa Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf da kuma Kwamishinan Ciniki da Masana’antu na Kano da ɗaukacin masu ruwa da tsaki wajen samun nasarar wannan zaɓe musamman shugaban hukumar tattara Haraji na jahar Kano Dakta Zayyad a zauna da su shugabanin kasuwanni don fuskantar juna yadda za a biya haraji daidai gwargwadon samun ɗan kasuwa ba tare da an tozarta shi ba.
