Da Ɗumi-Ɗumi: Kotun Ƙoli ta tsige Julius Abure a matsayin shugaban Jam’iyyar LP

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

A yau ne Kotun Ƙoli ta soke hukuncin Kotun Ɗaukaka ƙara a Abuja, wanda ke tabbatar da shugabancin Julius Abure a Jami’iyyar LP.

A wani hukuncin tawagar alƙalai biyar, kotun ta ce ta Ɗaukaka ƙara ba ta da hurumin ayyana Abure a matsayin shugaba, la’akari da cewa ƙarar ya na magana ne akan shugabancin jam’iyyar.

Kotun ta ce matsalolin da suka shafi shugabanci, abubuwa ne na cikin gida, ta na mai cewa tuni wa’adin Abure ya ƙare.

sauran bayanai za su biyo baya…

By Babaji