Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Wani magini mai suna Bayo Jeje ya tsere bayan da matarsa ta haifi ‘ya’ya uku rigis a wani asibiti mai zaman kansa da ke Igbokoda a ƙaramar Hukumar Ilaje ta jihar Ondo.
An ce Jeje ya tsere ne bayan wasu ungozoma da ma’aikatan jinya a asibitin sun shaida masa cewa mai-ɗakinsa, Iyanu Ehuwa Jeje ta haifi ‘ya’ya uku, dukkan maza.
Lamarin ya faru ne a ranar Talata, inda ya haifar da ruɗani a cikin asibitin Aribo da ke Ilaje yayin da ma’aikatan lafiya suka yi ta jimamin inda Jeje yake.
Majiyoyi a asibitin sun shaida wa Manhaja cewa mutumin ya bar matarsa da jariran da aka haifa a kwance a asibitin.
ɗaya daga cikin majiyoyin ta ce matar ta fara naƙuda ne da misalin ƙarfe 5 na safe, inda aka kai ta asibitin na Igbokoda, inda ta samu daɗewar naƙuda sakamakon rashin samun likita a bakin aiki.
“Bayan ciwon ta ya tsananta ne aka garzaya da ita asibitin Aribo, inda ta haifo ‘yan-uku.
“Tana haihuwar, mijin nata, wanda dama ya na ta iƙirarin rashin kuɗi, sai aka neme shi aka rasa, inda ya bar matar ta sa ba tare da kuɗin da za a biya don kula da jariran ba,” inji shi.
A halin da ake ciki, wani ma’aikacin lafiya a asibitin da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa Sanata Jimoh Ibrahim mai wakiltar mazaɓar Ondo ta Kudu a majalisar dattawa ya kawo ɗauki cikin lamarin.
Ya ce Sanatan na Ondo ya umarci ɗaya daga cikin masu taimaka masa, Juwon Ade-Aworetan Juwon, da ya kawo musu tallafin kuɗi cikin gaggawa.
