Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Shugaban ƙasar Amurka Donald Trump ya ƙaƙaba wa Nijeriya sabon harajin kashi 14.
Trump ya sanar da haka ne a ranar Laraba, inda ya ce daga yanzu za a caji kashi 14 kan duk kayayyakin Nijeriya da za su shiga ƙasar.
Sai dai mutane na ganin cewa wataƙila sabon harajin na Amurka ya shafi dangantakar ƙasashen biyu.
A cewar gwamnatin Trump, Nijeriya ita ma ta saka wa kayayyakin Amurka da za su shiga ƙasar harajin kashi 27, inda ta ce abin bai yi wa kasuwancin Amurka kyau ba.
Ana ganin cewa mai yiwuwa hakan ne ya sa Amurkar ita ma ta saka harajin ramako ga Nijeriya.
“Mun ƙaƙaba sabon harajin ga ƙasashen da ba sa yi mana daidai,” inji Trump.
