Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamnan Kaduna, Uba Sani, ya gargaɗi sosai ga sarakunan gargajiya da su guji ƙwace filayen domin wanzar da zaman lafiya a tsakanin al’umma a jihar.
Ya yi wannan gargaɗi ne a lokacin da ya kai ziyarar sallah ga sarkin Zazzau a fadarsa da ke garin Zariya a ranar Talata.
Gwamnan dai ya samu wakilcin Alhaji Muktar Shehu, mai ba wa gwamna shawara kan masarautu, wanda ya ce, gwamnatin jihar na ta samun ƙorafi kan ƙwacen filaye da hakimai ke yi a ƙauyuka.
Gwamnan ya jaddada cewa filaye dai na ƙarƙashin kulawar gwamnati, inda ya nuna muhimmancin bin ƙa’ida ga duk mai son mallakar fili ta hannun mahukuntan da suka dace domin samun zaman lafiya.
Ya buƙaci shugabannin gargajiya da su kula da batun zaman lafiya domin samun cigaba mai ɗorewa.
Ya ce, gwamnan yana ƙarfafa wa manoma guiwa domin su koma gona domin an samu ingantuwar tsaro a yankuna daban-daban.
A yayin da yake magana, sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli, ya taya al’umma murnar kammala azumin watan Ramadan tare da nuna farin cikinsa kan yadda ake ake gudanar da bikin sallah.
Tun da fari dai, sarkin Zazzau ya jaddada kiransa ga hakimai da masu unguwanni da su riƙa kwatanta adalci ga al’ummarsu.
Sannan ya gargaɗe su da su kaucewa wa haɗa kai da masu haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida a yankunansu.
Sarkin ya jaddada cewa akwai buƙatar samun sahalewar mahukunta kuma dole ne a sanar da masarauta kafin a fara.
Har’ila yau, ya gargaɗi masu unguwanni da su kaucewa ɗabi’ar son zuciya ta ƙwacen filayen da aka bai wa ma’aikatar kula da gandun daji tare da mayar da hankali ga kula da kadarorin masarauta.
“Duk wani fili mallakin gwamnati,” ya faɗa, yana mai jan hankali cewa duk wanda ya mallaki fili ba bisa ƙa’ida ba, zai fuskanci fushin hukuma.
Mai martaba sarki ya tuna wa masu riƙe da muƙaman gargajiya da ke da wani muƙami na daban da su ajiye ɗaya kamar yadda gwmnatin jihar ta buƙata ko su fuskanci kora ko hukunci.
Sannan ya buƙaci a samu haɗin kai a tsakanin sarkunan gargajiya domin tabbatar da zaman lafiya.
