La Liga ta ce, Barcelona ba ta da ikon yin rijistar ‘yan wasa Dani Olmo da Pau Victor, gabanin shawarar da hukumar wasanni ta Sifaniya (CSD) ta yanke kan cancantar ‘yan wasan biyu na doka wasa.
A watan Janairu Barcelona ta sanar da cewa an cimma yarjejeniyar sayar da manyan akwatina a filin wasa na Camp Nou, wanda a halin yanzu ake sake ginawa, wanda kuɗinsa ya kai Yuro miliyan 100 (dala miliyan 108), wanda ya ba su damar baje kolin kuɗi na sayen sabbin ‘yan wasa.
La Liga ta ce Barcelona ta yi amfani da wani mai binciken kuɗi da ba a bayyana sunansa ba tsakanin 31 ga Disamba zuwa 3 ga Janairu wanda ya rubuta yarjejeniyar a kan littattafan kulob ɗun, amma mai binciken su na yanzu ba ya saka ta a cikin bayanan kudi na wucin gadi na kulob ɗin na farkon kakar 2024-25.
A cikin wata sanarwa da La Liga ta fitar ta ce “Babu wani adadin daga (kwatin VIP) da aka rubuta a cikin asusun riba da asarar, saɓanin abin da kulob ɗin da mai binciken kuɗi suka tabbatar a lokacin cinikin,” inji La Liga a cikin wata sanarwa.
La Liga ta ce suna kai rahoton mai binciken da Barcelona ta yi amfani da su a tsakanin 31 ga Disamba zuwa 3 ga Janairu ga Cibiyar Aiki.
Barcelona ta ƙi cewa komai lokacin da kamfanin dillancin labaran Faransa AFP ya tambaye ta game da lamarin.
