Shugaban Hukumar Wasanni ta ƙasa (NSC) Mallam Shehu Dikko, a madadin ɗaukacin masu ruwa da tsaki a harkokin wasanni, ya miƙa godiyarsa ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa rattaba hannu a kan ƙudirin dokar hana amfani da kwayoyi masu ƙara kuzari.
A cewar shugaban NSC da ya rattaba hannu kan ƙudirin dokar, wanda aka shafe kusan shekaru 20 ana gudanar da shi, a cikin doka yana ƙarfafa niyyar shugaba Tinubu don tabbatar da cewa al’ummar ƙasar sun yi daidai da ƙa’idojin yaai da ƙwayoyin ƙara kuzari a duniya da kuma ci gaban wasanni gaba ɗaya.
A cewarsa, “Ina godiya da godiyata ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya gaggauta sanya hannu kan wannan ƙudiri, tun daga rana ɗaya, shugaban ƙasa bai taba ɓoye burinsa na ganin an aiwatar da hakan ba, ya kuma umurci dukkan ɓangarorin da abin ya shafa da su gaggauta aiwatar da ƙudurin, domin tabbatar da an kammala ƙudirin bayan ya shafe kusan shekaru ashirin, inda akwai wasiyya, to dole ne a samu hanyar da za a bi domin kawo ƙarshen wannan ƙudiri.
“Duk nasarorin da muka samu a cikin wannan dan ƙanƙanin lokaci ya rage ga goyon bayan shugaban kasa da karfafa gwiwa. Wannan wata alama ce da ke nuna goyon bayan shugaban kasa da muke samu.”
Ya ci gaba da cewa, “Haƙiƙa, dole ne in gode wa sauran masu ruwa da tsaki da suka yi aiki tukuru domin ganin an kammala hakan kamar yadda mai girma shugaban ƙasa ya umarce mu, na tuna lokacin da aka nada mu, daya daga cikin abubuwan da shugaban ƙasa ya ba da umurni nan da nan shi ne tabbatar da ganin an kawo ƙarshen dokar hana shan kwayoyi masu ƙara kuzari a nan take, don haka nan take muka shiga aiki tare da duk ɓangarorin da abin ya shafa daga ofishin lauyan gwamnati da na majalisar dattawa da na majalisar wakilai ta tarayya da na ministocin harkokin wasanni da na majalissar wakilai ta tarayya. Magatakarda na Majalisar Dokoki ta ƙasa, wakilan shari’a da kuma jami’an WADA.
Dokar ta yi amfani da Yarjejeniyar ƙasa da ƙasa ta Yaƙi da ƙwayoyin ƙara Kuzari a Wasanni tare da kafa wata hukuma mai zaman kanta da ke da alhakin aiwatar da ƙa’idojin yaƙi da shan kwayoyi na duniya da ƙa’idojin ƙasa da ƙasa da Nijeriya ta yi wa rajista.
Abu mafi muhimmanci shi ne, wannan doka ta kafa Cibiyar Yaƙi da ƙwayoyin ƙara Kuzari a Nijeriya, ci gaban da ya faranta ran Mallam Dikko.
