
Daga BELLO A. BABAJI
Babbar Kotun Koriya ta Kudu ta tabbatar da hukuncin tsige Shugaba Yoon Suk Yeol na ƙasar bayan watanni ana fama da rikicin siyasa, lamarin da ya bada damar gudanar da sabon zaɓe a ƙasar.
A ranar 3 ga watan Disambar 2024 ne ƴan majalisar dokokin ƙasar suka dakatar da shi daga shugabancin ƙasar sakamakon samun sa da laifin lalata tsarin jagorancin mulkin farar hula da wasu manyan laifuka.
Ana sa ran gudanar da babban zaɓen ƙasar nan da kwanaki 60 bayan hukumomi sun sanar da rana.
AFP ta ruwaito cewa, magoya bayan Yoon sun yi yunƙurin kashe alƙalan da suka zartar da hukuncin, inda ganin haka ya sa aka tsaurara matakan tsaro wajen ƙara adadin dakarun da aka zuba.
Alƙalan sun tabbatar da cewa, Yoon ya saɓa wa dokokin ƙasa da na tsarin gudanar da demokraɗiyya.
Daga cikin abinda ya yi na saɓa wa doka shi ne tura sojoji zuwa majalisa domin hana ƴaƴanta kaɗa kuri’un ƙin amincewa da tsare-tsarensa da kuma zamba cikin aminci da ya yi wa al’ummar ƙasar.
Tuni jam’iyyun adawa suka jinjina tare nuna farin cikinsu ga hukuncin tsige Shugaba Yoon Suk.
Bayan hukuncin ne Yoon ya fitar da wata sanarwa, inda ya ke bada haƙuri ga al’umma akan rashin cika alƙawarin da ya ɗaukar masu.
