
Daga BELLO A. BABAJI
Babban Kamfanin Raba Wutar lantarki na Ƙasa, TCN ya ce ayyukan lalata kayayyakin lantarki daga masu ayyukan haramtattun haƙar ma’adanai da wasu ɓata-gari a Nijeriya na barazana ga ɗorewar lantarki ga al’ummar ƙasar.
Ya ce, lallai sai an kawo ƙarshen ayyukan nasu kafin za a daina fuskantar ɗaukewar wuta akai-akai ganin yadda tashoshi da layukansa ke samun tsaiko.
Manaja Janar na Shiyyar Enugu, Dakta Thomas Inugonum ya garzaya wata tasha da manema labarai, inda ya nuna masu wajen da aka haƙa wani sashi na layukan, waɗanda tsawa da iska ka iya ɗaiɗaita su.
Ya ce, har ta kai ga mutanen sun cire dutsen da aka sanya a kusa da kewayen tashoshin a matsayin alama da ke nuna cewa ba a so a je wajen ba tare da izini ba.
Ya bayyana cewa, matuƙar ba a dakatar da su ba akwai yiwuwar a samu ɗaukewar wuta na tsawon lokaci kamar yadda aka samu a Arewa a kwanakin baya.
Ya kuma shaida wa manema labaran cewa, an sace kayan aikin wata ƙaramar tasha da aikinta ya kai kaso 90 da kammalawa, wanda adadin kuɗinsu ya kai Naira biliyan 20 a shiyyar.
A saboda haka ne ya ce, suna ƙoƙarin ganin an kammala sauran ayyuka wasu tashoshi a shiyyar cikin ƙanƙanin lokaci.
