
Daga BELLO A. BABAJI
Babban Kamfanin Man fetur na Ƙasa, NNPCL, ya naɗa tawagar manyan ma’aikata da ya ƙunshi jami’ai guda takwas.
Lamarin ya biyo bayan naɗa sabon Shugaban Kamfanin (GCEO) ne da kuma tawagar daraktoci (BoD).
Jami’in yaɗa labaran kamfanin, Olufemi Soneye ya bayyana hakan a wata sanarwa, ranar Juma’a, inda ya ce tawagar za ta fara aiki ne a nan take.
Shugaban Kamfanin, Mista Bashir Bayo Ojulari, shi zai jagoranci tawagar; sai babban jami’in ayyuka, Rowland Ewubare; Adedapo Segun a matsayin babban jami’in kuɗi; da Olalekan Ogunleye a matsayin babban mataimakin shugaba a ɓangaren makamashi.
Sauran sun haɗa da: Udy Ntia a matsayin babbar matiamakiya ɓangaren ‘Upstream’; Mumuni Dangazau a matsayin babban mataimakin shugaba ɓangaren tacewa na ‘Downstream’; sai Sophia Mbakwe – babbar mataimakiyar shugaba kan harkokin kasuwanci; da kuma Adesua Dozie a muƙamin Sakatariya kuma babbar jami’ar shari’a, kamar yadda Kakakin ya bayyana.
