Gwamnan Kebbi ya dakatar da babban sakatare bayan ya ce jihohin Arewa ke da mafi yawan ƴan luwaɗi da ƴan maɗigo

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Gwmanan Jihar Kebbi, Nasir Idris ya dakatar da babban sakataren ma’aikatansa, Dakta Nasiru Abubakar Kigo, kan cewa Jihohin Kebbi da Sakkwato ne suke da mafi yawan mutanen da ke harkokin luwaɗi da maɗigo.

A baya ne sakataren ya gudanar da lakca a wani taron addini, inda ya ce jihar ta na da adadi mai yawa na ƴan luwaɗi (guda 15,979) da ƴan maɗigo (guda 18,567).

Ya ce, Sakkwato ta na da ƴan luwaɗi 9,978, yayin da ƴan maɗigo suka kai guda 10,456, lamarin da ya sa ta zama ta uku a Nijeriya a yawan adadin masu irin aikin.

Da fari, gwamantin jihar ta nesanta kanta daga ikirarin Daktan da kuma ƙaryata su, kana daga bisani a ranar Juma’a, cikin wata sanarwa da Sakataren yaɗa labaran gwamnan, Ahmad Idris ya fitar, gwamnan ya sanar da dakatar da Dakta Kigo.

A wata takarda, Shugaban ma’aikatan jihar, Malami Shekare ya ce kalaman Daktan sun saɓa wa dokokin gudanar da ma’aikata, waɗanda suka bayu zuwa ga ɓata sunan jihar.

By Babaji