Dalilin da ya sa za a saida fetur N750 kafin Disamba – Shugaban NIPSS

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUGAMMAD

Cibiyar Nazarin Tsare-tsare ta ƙasa (NIPSS) ta bayyana cewa, ayyukan matatar Dangote da wasu da suka shigo harkar, ya kamata ‘yan Nijeriya su yi tsammanin faɗuwar farashin man fetur.

An sayar da samfurin a kan aasa da N200 kowace lita kafin a cire tallafi; A halin yanzu ana sayar da shi kusan N930 kan kowace lita, ya danganta da wuri.

Sai dai, Darakta-Janar na NIPSS, Ayo Omotayo, ya ce yayin da cire tallafin man fetur da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta yi ya haifar da hauhawar farashin kayan masarufi, akwai kwanaki masu kyau na nan gaba.

“Yayin da aka cire tallafin a farko, mun samu matatar Dangote. Muna da sauran matatun mai. Matatar man da ke Fatakwal ta ci gaba da aiki har tsawon kwanaki 110. Wannan shi ne ribar da aka samu na ɗan gajeren lokaci,” inji Omotayo a ranar Talata a wani shirin gidan talbijin na Channels.

“Muna sayen mai ɗan kaɗan ne, amma kamar yadda muka yi hasashe a cibiyar ta ƙasa cewa idan muka ci gaba da abin da muke yi a halin yanzu, man fetur da kansa zai sauko, muna dubansa ya sauko ƙasa da N750 kafin ƙarshen shekara.

“Kuma tabbas, mu mun yi imanin cewa, har yanzu kuɗin ƙasashen waje zai ragu zuwa kusan 1.3 kafin ƙarshen shekara, kuma za a ci gaba da kasancewa a haka yayin da matatun man ƙasar suka fara aiki, za mu zama masu fitar da kayayyaki zuwa ƙasashen waje a nan gaba.

“Ribar da aka samu a wannan lokaci kaɗan ne, amma nan gaba kaɗan, za mu rama duk wani sadaukarwa da muka yi a yau a matsayinmu na ’yan Nijeriya.

Matakin na Shugaba Tinubu ya kawo ƙarshen shirin tallafawa farashin mai. Shekaru da dama, Gwamnatin Tarayya ta yi musayar ɗanyen man fetur da man fetur da ta ke ba da tallafi ga kasuwannin cikin gida, lamarin da ya jawo taɓarɓarewar kuɗaɗen shiga, da musayar kuɗaɗen waje da kuma bayar da gudunmuwa ga basussuka.

By ukarofi