Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Masu ruwa da tsaki a harkar sufurin jiragen sama, da suka haɗa da Hukumar Kula da Harkokin Sufurin Jiragen Sama watau NCAA a ’yan kwanakin nan sun bayyana damuwarsu kan ƙaruwar satar da ake yi a jiragen cikin gida, da suka shafi fasinjoji.
An ruwaito cewa, fasinjoji a cikin ‘yan kwanakin nan sun koka tare da bayar da rahoton cewa kayayyakin da ake ajiyewa a wurin ajiya suna ɓata.
Sau da yawa matafiyi ba ya gane cewa wani abu ya ɓace sai daga bayan.
Hukumar Kula da Harkokin Sufurim Jiragen Sama ta Nijeriya (NCAA) ta taaaita ayyukan zirga-zirgar jiragen sama na ƙasa da ƙasa da na cikin gida daga watan Janairu zuwa Disamba 2024, ta ba da sunayen kamfanonin jiragen sama da adadin ƙorafin sata ya yi yawa a kan su.
Ga kamfanonin jiragen sama na ƙasa da ƙasa, rahotanni sun nuna cewa Royal Air ne ke kan gaba a yawan ɓacewar kayan da kuma ƙararrakin rashin jin daɗi tare da ƙararraki 58 daga cikin jirage 473 da aka yi a cikin lokacin. Jirgin ƙatar Air ya biyo bayan ƙoƙari 47 daga cikin jirage 1,375.
Egypt Air 47 daga cikin jirage 820 da kuma Ethiopian Air sun sami ƙararraki 38 daga cikin jirage 1,197 da aka yi. Turkish Airline 28 daga cikin jirage 582 da Taac Angola sun sami kararraki 23 daga cikin 255 da aka yi.
A fagen cikin gida, Air Peace ne ke jagorantar yawan samun ƙorafin ɓacewar kaya da 404 daga cikin jirage 15,413; Arik Air ya biyo baya da 396 daga cikin jirage 10,699; Dana Air 316 daga cikin jirage 1,446, Aero Contractors 270 cikin 4,559, Ibom Air 238 daga cikin jirage 7,856, Green Africa 170 daga cikin 4,215, United Nigeria Airlines 131 daga cikin 7,794
Sauran sun haɗa da Maɗ Air mai ɗauke da ƙararraki 84 daga cikin jirage 4,783, Overland 52 daga cikin jirage 3,407 da NG Eagle 35 daga cikin jirage 1,166.
Don rage satar da ake samu a cikin jirage, lokacin da fasinjoji ke shiga jirgin, ana shawarce su da su ajiye jakunkunan su da suke ɗauke da su a cikin wani zaki na sama kai tsaye a kan hanyar da suke zaune. Ta wannan hanyar, za su iya gani nan da nan idan wani ya yi ƙoƙari ya ɗauki wani abu.
Lokacin da fasinjoji suka sanya jakarsu a cikin ɗakin, ana ba su shawarar su juya ta. Hakan zai sa ɓarawo ya yi wahala ya ɗauki abubuwa daga cikin jakar ba tare da cire shi daga ɗakin ba.
