Wani yaro ɗan shekara huɗu da ya kira ’yan sandan ta wayar salula a yankin Mount Pleasant a ƙaramar Hukumar Charleston Jihar South Carolina da ke Amurka, ya ce, mahaifiyarsa ta shanye masa ‘ice cream’ ɗinsa kuma yana buƙatar a hukunta ta, a kai ta gidan yari saboda aikata hakan.
A cewar ’yan sanda yaron ɗan shekara huɗun ya yi kururuwa, inda ya kira ’yan sanda bayan mahaifiyarsa ta shanye masa ice cream ɗinsa.
Al’amarin ya faru ne a cikin a garin Mount Pleasant, Wisconsin, mai nisan kilomita bakwai, yamma da Racine, lokacin da yaro ɗan shekara huɗu ya tuntuɓi ‘yan sanda, inda ya ce, mahaifiyarsa ba ta kyauta masa ba, a cewar wata sanarwa da ’yan sandan ƙauyen Mount Pleasant suka fitar.
“An aika jami’an ’yan sanda, wato Gardinier da Ostergaard don amsa kiran mai ƙorafin neman agajin jami’an 911, wanda ya bayyana cewa, mahaifiyarsa ba ta kyauta masa kuma yana buƙatar a kai ta gidan yari”, inji hukumomi.
Lokacin da jami’ai suka isa gidansu, yaron ya ce, mahaifiyarsa ta shanye masa ‘ice cream’ ɗinsa kuma yana buƙatar a ka ita gidan yari saboda aikata hakan.
Daga bisani ya kuma shaida wa ’yan sanda cewa, ba ya son a kai mahaifiyarsa gidan yari kawai, yana son a biya shi ice cream ɗin da ta shanye masa ne.
Jami’an ’yan sandan da suka amsa kiran, ba su kaɗai ne suka gano abin dariya game da lamarin ba.
Jami’an ’yan sandan da suka ziyarci gidan su yaron sun ɗauki hoto tare da yaron mai shekara 4 bayan an warware matsalar, inda suka samu damar yin barkwanci.
