Kisan Filato: ACF ta buƙaci a sanya dokar ta-ɓaci a yankunan da iftila’in ya shafa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

A ranar Lahadi ne Ƙungiyar Mashawartan Arewa (ACF), ta bayyana takaicinta game da kashe-kashen al’umma da ake yi a wasu yankunan Jihar Filato, inda ta yi kira da a sanya dokar ta-ɓaci a dukkanin sassan da ƴan ta’adda suka addaba a Arewacin Nijeriya.

Haka kuma ACF da Ƙungiyar Kiristocin Nijeriya (CAN) sun yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta ƙara ƙaimi wajen yaƙar ayyukan ta’addanci a shiyyar.

Hakan ya biyo bayan ikirarin Gwamnatin Tarayyar ne na cewa an sami nasara a yaƙi da ta’addanci da samar da tsaro da kaso 90.

Gwamantin ta kuma tabbatar da cewa za ta cigaba da ƙoƙarin kawo ƙarshen ta’addanci da samar da zaman lafiya mai ɗorewa a Nijeriya.

A sanarwar da Sakataren yaɗa labarai na ACF, Farfesa Tukur Muhammad Baba taya fitar, ta yi alhinin mace-macen da aka samu na rayukan al’umma a sakamakon harin da wasu mahara suka kai wa ƙauyuka a Ƙaramar Hukumar Ɓokkos dake Filato.

Ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta yi abinda ya dace wajen ganin an kawo ƙarshen faruwar irin haka a nan gaba tare da hukunta waɗanda aka samu da hannu a laifin.

Ta kuma miƙa gaisuwar ta’aziyyarta ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu a yayin iftila’in da Gwamnatin jihar da kuma fatan samun waraka cikin ƙanƙanin lokaci ga waɗanda suka samu raunuka.

By Babaji