Kisan Bokkos: Tinubu ya gargaɗi masu son tayar da rikici a Filato

Spread the love

Daga HABU ƊAN SARKI a Jos

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gargaɗi masu shirin tayar da fitina a wasu sassan Jihar Filato su yi wa kansu faɗa, domin kuwa gwamnati ba za ta lamunci kisan gilla da kai hare-hare kan waɗanda ba su ji ba ba su gani ba. Don haka ya ce, fitinar da ake fuskanta ta rashin zaman lafiya a jihar fiye da shekaru ashirin ya kamata a kawo ƙarshen ta.

Shugaba Tinubu ya bayyana haka a cikin saƙon da ya aike ga gwamnati da al’ummar Filato ta bakin mai mai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribaɗu, yayin ziyarar aiki ta wuni ɗaya da ya kawo jihar.

Bayan ganawarsa da Gwamnan Jihar Filato Caleb Mutfwang da babban kwamandan runduna ta uku, kuma mai kula da rundunar haɗin gwiwa ta OPSH, Manjo Janar Oyitayo Oyinlola, inda ýa isar da ta’aziyyar shugaban ƙasa ga gwamnati da al’ummar Filato, Ribaɗu ya shaida wa manema labarai cewa, gwamnatin tarayya da haɗin gwiwar gwamnatin jihar za su cigaba da ƙoƙari don samar da zaman lafiya mai ɗorewa, ba a Jihar Filato kaɗai ba har ma dukkan sassan ƙasar nan.

Ya ce, jami’an tsaron Nijeriya na samun gagarumar nasara a yaƙin da suke yi da ýan ta’adda da masu riƙe da makamai, kuma ana hukunta su daidai da abin da suka aikata. Ko bayan harin da aka kai wasu ƙauyuka a ƙaramar hukumar Bokkos, an kama mutane da dama kuma ana nan ana cigaba da bincike.

Ribaɗu ya ƙara da cewa, shugaban ƙasa ya damu sosai da al’amarin rashin tsaro da yake faruwa a Jihar Filato, kuma ya ba da tabbacin cewa, waɗanda suka aikata wannan ta’addanci ba za su tafi haka a banza ba, za a nemo su a duk inda suke, da duk masu mara musu baya, har sai sun ɗanɗana kuɗarsu.

“Za mu yi duk mai yiwuwa don ganin cewa an dawo da dawwamammen zaman lafiya da cigaban walwalar jama’a, ta yadda jama’a za su ji daɗin rayuwa ba tare da fargabar komai ba.”

Da yake ƙara jan hankalin ýan jarida game da muhimmancin tantance bayani a rahotanninsu da haƙƙin su na nuna kishin ƙasa, Malam Nuhu Ribaɗu ya ƙaryata irin rahotannin da wasu jaridu ke bayarwa game da kashe-kashen da aka yi a Bokkos, musamman game da adadin mutanen da ake cewa an kashe.

Ya ce, Lissafin da ake bayarwa ba gaskiya ba ne, jami’an tsaro na kan haɗa adadin da aka kashe da waɗanda suka jikkata. Ko da rai ɗaya ne aka rasa gwamnati ba za ta lamunci kisan gilla ba. Faɗar gaskiya kan abin da ya faru zai taimaka wajen kawo waraka ga mutane da ke fama da haushi a zukatan su. Fitar da rahoto mai inganci zai taimaka wajen kawo zaman lafiya da tsaro a Filato da ƙasa baki ɗaya.

Mai ba da shawara kan harkokin tsaron, ya kuma yabawa jami’an tsaro da ke aiki ba dare ba rana, domin dawo da zaman lafiya da tsaro a yankin da ke ƙarƙashin kulawarsu, da suka haɗa da Bauchi, Kudancin Kaduna, da Taraba.

Idan za a iya tunawa a tsakanin ranakun 27 ga watan Maris zuwa 2 ga watan Afrilu, 2025 wasu mahara suka kai munanan hare-hare a ƙauyukan Hurti da Tadai da Gwande da Manguna da kuma Daffo duk a ƙaramar hukumar Bokkos da ke Jihar Filato.

Jihar Filato ta daɗe tana fama da rikice-rikice masu nasaba da ƙabilanci da addini, wanda ya ke haifar da asarar rayuka da dukiya mai ɗimbin yawa.

Malam Nuhu Ribaɗu ya kuma ziyarci gidan Shugaban majalisar malamai ta ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’a Wa Iƙamatus Sunnah, Sheikh Sani Yahaya Jingir, domin yi masa ta’aziyyar rasuwar babban na hannun damansa, Sheikh Sa’idu Hassan Jingir. Sannan ya je gidan shugaban al’ummar Jos kuma Turakin Jos Alhaji Garba Abdulƙadir inda nan ma ya yi masa ta’aziyya bisa rashin da aka yi masa.

By ukarofi