An yaba wa Shettima bisa rawar da ya ke takawa wajen yaƙi da ƙarancin abinci a Nijeriya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Mataimakin Shugaban ƙasa, Kashim Shatima ya karɓi baƙoncin tawagar gidauniyar tallafi ta Big Win bisa jagorancin Shugabarta, Jamie Cooper, yayin wata ziyarar ban girma da suka kawo Fadar Shugaban Ƙasa.

Hakan ya biyo bayan rawar da mataimakin shugaban ƙasar ya ke takawa ne wajen yaƙi da matsalar ƙarancin abinci mai gina jiki da Kuma buƙatar haɗin gwiwa da Gwamnatin Tarayya.

Da ya ke jawabi, Shatima ya bayyana cewa, hangen nesa da jagoranci na gari na Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, nan ba da jimawa ba zai sauya Nijeriya zuwa mataki mai inganci da zai taimaki al’umma.

Ya kuma yi maraba da ziyarar da Gidauniyar ta kawo tare da alkawarin yin aiki tare da Gwamnatin Tinubu, domin sabonta Ajandar Fata Nagari musamman a fannin kiwon lafiya,ilimi da sauran muhimman sassa na bunkasa tattalin arziƙi.

By Babaji