Masu zanga-zanga sun yi watsi da gargaɗin ƴan sanda a Legas, Abuja, Ribas da wasu jihohi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

A ranar Litinin ne wasu masu zanga-zangar tafiyar ‘Take-it-back’ suka yi buris da gargaɗin rundunar ƴan sanda na hana su fitowa, inda suka yi dandazo a wasu titinan jihohin Abuja, Legas, Ribas, Oyo da sauran su.

Da fari dai rundunar ta yi kira ga ƴan tawagar tafiyar ne da su soke batun yin zanga-zangar, inda ta ce lokacin da suka zaba bai dace da halin da ake ciki ba.

Saidai, duk da haka tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa kuma ɗan kishin al’umma, Omoyele Sowore ya yi watsi da gargaɗin ƴan sandan, inda ya ce an shirya zanga-zangar ne a ranar Litinin da nufin hana ranar ƴan sanda yin tasiri.

Wasu daga cikin dalilan yin zanga-zangar sun haɗa da halin da tattalin arziƙin ƙasa ya ke ciki da kuma dokar ta-ɓaci da Shugaba Bola Tinubu ya sanya a Jihar Ribas da sauran su.

Al’umma sun gudanar da zanga-zanga a Ibadan, babban birnin jihar Oyo, inda aka baza jami’an ƴan sanda don tabbatar da kiyaye doka da oda.

A Fatakwal kuma, sai da ƴan sanda suka fesa hayaƙi mai sanya hawaye sakamakon yunƙurin haddasa fitina da sunan zanga-zangar.

Lamarin da ya sa ƴan sanda suka yi duka ga wasu daga cikin ƴan zanga-zangar har da ƴan jaridar da ke tattara labarin.

By Babaji