Lakurawa sun kashe ƴan bijilante 13 a Kebbi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Kimanin ƴan bijilante 13 ne mayaƙan Lakurawa suka kashe a wani hari da suka kai a ƙauyen Morai dake Ƙaramar Hukumar Augie a Jihar Kebbi.

Wani shaida mai suna Alhaji Augie, ya bayyana cewa, lamarin ya auku ne a lokacin da ƴan bijilanten suka yi ƙawanya wa yankin bayan samun wani rahoton sirri game farmakin ƴan ta’addar.

Ya ce, a lokacin da mayaƙan suka hallara, sun yi yunƙurin satar dabbobi ne, inda ƴan bijilanten suka mayar da martani da nufin ƙwato dabbobin. Saidai mayaƙan sun kewaye su sakamakon kere su a adadi da makamai.

Ya kuma ce, an yi wa gawarwaki shida salla kamar yadda addinin musulunci ya tanada, yayin da ake cigaba da neman sauran waɗanda iftila’in na ranar Lahadin ya afka musu.

Zuwa lokacin kammala rahoton, ba a samu kakakin rundunar ƴan sandan jihar a waya ba, kuma bai bada amsa ga saƙonnin da aka aika masa ba.

By Babaji