
Daga BELLO A. BABAJI
A ranar Litinin ne Nijeriya da Sweden suka sanar da ƙarfafa alaƙa kan harkokin da suka shafi tattali musamman wajen amfani da fasahar zamani don inganta rayukan al’ummominsu.
Lamarin ya biyo bayan ziyarar da Gimbiyar ƙasar, wato ‘Victoria of Sweden’ zuwa Fadar Shugaban ƙasa dake Abuja, a wani ziyarar kwanaki uku don haɓaka harkokin siyasa da tattalin arziƙin ƙasashen biyu.
Ya ce, ziyarar ta kuma ƙunshi haɗa hannu a tsakanin su wajen inganta cibiyoyin kasuwanci da ƙarfafa alaƙar al’adu da ke tsakaninsu.

Mai Martaba, Gimbiya Victoria ta ce, Nijeriya da Sweden sun yi tarayya a ɓangarori da dama, ta na mai cewa hakan abu ne da ya kamata a yi shi tun da jimawa.
Mataimakin Shugaban ƙasar ya kuma yi kira ga manyan ƴan kasuwa da su yi amfani da damar hakan musamman ganin yadda matasa ke da buƙatar a inganta su ta fuskar ci-gaban zamani.
Kazalika, ya ce Gwamnatin Tarayya za ta bada dukkan haɗin kan da ake buƙata don ganin an cimma a yayin gudanar da al’amuran da suka shafi sabuwar alaƙar.

