Gwamnatin Tinubu ta zaɓi 7 ga Afrilu a matsayin ranar tunawa da ƴan sanda

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Mataimakin Shugaban ƙasa, Kashim Shettima ne ya bayyana hakan a yayin da ya ke wakiltar Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu a wajen bikin ranar ƴan sanda karo na farko a dandalin Eagle Square.

Bikin shine irinsa na farko tun bayan da Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta ayyana ranar 7 ga Watan Afrilun kowace shekara a matsayin ranar tunawa da irin gudunmawar da jami’an ƴan sanda ke bayarwa wajen wanzar da tsaron ƙasa.

Da ya ke jawabi yayin gudanar da taron Sanata Kashim Shatima ya jaddada kudurin Gwamnatin Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinibu na horar da Jami’an ‘Yan Sanda tare da samar musu da kayan aiki na zamani don yakar manyan laifuka a Najeriya

Shattima ya kuma tabbatar wa al’ummar Nijeriya cewa Gwamnatin Tarayya za ta yi duk mai yuwuwa wajan tabbatar da ingancin aikin ƴan sanda da kuma tabbatar da kawo ƙarshen matsalar tsaro a Najeriya.

By Babaji