Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa gwamnatinsa na da cikakken ƙuduri wajen sauya fasalin rundunar ‘yan sanda ta ƙasar, ta yadda za ta kasance mai ƙwarewa, mai amfani da sabbin fasahohi, da kuma isassun kayan aiki domin yaƙi da laifuka a Najeriya.
Shugaban ya bayyana haka ne a ranar Litinin yayin bikin farko na ranar ‘yan sanda ta ƙasa da aka gudanar a dandalin Eagle dake Abuja, inda ya sanar da 7 ga Afrilu a matsayin ranar bikin ‘yan sanda na ƙasa a kowace shekara.
Shugaban ya ce: “Tsaron Najeriya na da matuƙar muhimmanci ga cigaban ƙasa. Wannan sauyi yana farawa ne da tabbatar da cewa rundunar ‘yan sandanmu na da horo mai inganci, kayan aiki na zamani, da kuma walwala. Mun ɗauki alƙawari cewa albashi, gidaje, lafiyar jiki da ilimi ga iyalan jami’an ‘yan sanda za su samu kulawa ta musamman.” Ya ce gwamnatin tarayya ta kammala shirye-shirye don inganta rayuwar jami’an ‘yan sanda ta hanyar samar da ingantattun kayan aiki da yanayin aiki.
Shugaba Tinubu, wanda mataimakinsa, Kashim Shettima, ya wakilta, ya jaddada cewa gwamnati ba za ta bar ko da dutse ɗaya ba wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin ‘yan ƙasa, da kuma magance matsalolin tsaro kamar ‘yan bindiga, ta’addanci da garkuwa da mutane. Ya kuma yaba da irin rawar da ‘yan sanda ke takawa a kare dimokuraɗiyya da tsaron lafiyar al’umma, yana mai cewa sun cancanci a yaba musu da girmamawa.
A nasa jawabi, Sufeto Janar na ‘yan sanda, Kayode Egbetokun, ya ce ranar ‘yan sanda na ƙasa dama ce ta tunawa da waɗanda suka sadaukar da rayukansu, da kuma ƙara ƙarfafa gwiwar jami’an da ke bakin aiki a faɗin Najeriya da ma ƙasashen waje. Ya bayyana cewa gyare-gyaren da ake yi a rundunar suna da nufin gina runduna da za ta kasance abin amincewa, wacce za ta yi aiki da ƙwarewa tare da kare haƙƙin ɗan Adam da tabbatar da zaman lafiya a ƙasa.
