Daga USMAN KAROFI
Mataimakin shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bayyana aniyar Nijeriya na ƙara ƙarfafa hulɗar kasuwanci da kamfanin fasaha na ƙasar Sweden, Ericsson, ta hanyar fara aiwatar da yarjejeniyar da aka ƙulla tsakanin ɓangarorin biyu a shekarar 2024. Ya bayyana haka ne yayin da ya karɓi baƙuncin tawagar kamfanin a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, ƙarƙashin jagorancin babban mataimakin shugaban Ericsson na kasuwannin Turai, Gabas ta Tsakiya da Afirka, Mista Patrick Johansson.
Shettima ya ce kamfanin Ericsson wani ɓangare ne na tarihin ci gaban fasaha a Najeriya, domin kuwa shi ne ya shimfida tubalin da sauran manyan kamfanonin fasaha suka biyo baya. Ya yaba da yadda kamfanin ke zuba jari a cibiyoyin ƙirƙire-ƙirƙire da kuma tallafawa ƙananan ‘yan kasuwa a Najeriya, yana mai cewa hakan wata alama ce ta ci gaba da haɗin gwiwa da goyon baya daga Ericsson.
Mataimakin shugaban ƙasar ya buƙaci kamfanin Ericsson da sauran masu zuba jari da su ci moriyar dimbin al’umma matasa masu fahimtar fasaha a Najeriya. Ya ce, “Muna da alaƙa mai ƙarfi da ƙasar Sweden da kamfaninku. Muna da yawan jama’a da ke da ƙwarewa a fannin fasaha. Wasu daga cikin manyan kamfanoni masu ci gaba da daraja a Afirka suna da asali daga Najeriya. Makomar Afirka tana cikin Najeriya.”
A nasa ɓangaren, Patrick Johansson ya bayyana cewa akwai buƙatar ci gaba da ƙarfafa alaƙa tsakanin Najeriya da Ericsson ta hanyar bunƙasa ƙirƙire-ƙirƙire daga tushe da kuma tallafawa masu ƙananan sana’o’i. Haka zalika, Majda Lahlou Kassi, wanda shi ne mataimakin shugaban Ericsson a yankin Yammacin da Kudancin Afirka, ya ce Najeriya tana da matsayi na musamman a tarihin kamfanin, kuma suna alfahari da dangantaka da ƙasar da kuma damar da ke akwai wajen inganta al’adar dijital a tsakanin al’umma.
