
Daga BELLO A. BABAJI
Ma’aikatar Harkokin Waje ta ƙaryata rahoton da ke cewa ƙasar Saudiyya ta haramta bada bisa ga Nijeriya da wasu ƙasashe 13.
A wata sanarwa da mai taimaka wa ministan ma’aikatar kan harkar yaɗa labarai, Alƙasim Abdulƙadir ya fitar, ya ce hukumomin Saudiyya sun ƙaryata batun da ake cigaba da yaɗawa acikin al’umma.
Ya ce, batun cewa Nijeriya ta shiga sahun ƙasashen da aka haramta ba su bisar shiga ƙasar, wanda zai fara aiki daga ranar 14 ga watan Afrilu, ba gaskiya ba ne.
Cibiyar Walwalar al’umma ta Saudiyya ta ce babu wata magana mai kama da haka, ta na mai cewa batun tafiya da ake shirye-shirye akan sa a yanzu shi ne na zuwa aikin hajji.
Saidai, don ƙaurace wa kokwanto, batun taiƙace zirga-zirga a ƙasar shi ne ga masu zuwa yawon buɗe ido. Wato an haramta wa ire-iren su yin aikin hajji, shiga ko zama a Makka daga ranar 29 ga Afrilu har zuwa 11 ga Yuli, 2025 (bayan kammala aikin hajji).
Bisar da aka amince da ita kaɗai, ita ce ta zuwa aikin hajji a halin yanzu.
Don haka ne Ma’aikatar ta yi kira ga al’umma da su riƙa tantance labari daga hukumomin da abu ya shafa gabannin ɗaukar mataki.
