
Daga BELLO A. BABAJI
Fadar Shugaban Ƙasa ta ƙaryata jita-jitar cewa an maye gurbin Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu.
Ta bayyana batun a matsayin labarin bogi, inda ta ce labarin ya na yawo a Soshiyal Mediya kan cewa Shugaba Bola Tinubu ya maye gurbin Farfesan.
Saidai, Mai taimaka wa shugaban ƙasa kan harkar yaɗa labarai ta kafar zamani, O’tega Ogra, ya bayyana cewa, babu ƙamshin gaskiya a cikin hakan ya na mai kira ga al’umma da su ƙaurace wa batun, a wani jageren saƙo da ya fitar.
Ya kuma ce, matuƙar hakan ya faru, za a samu sanarwa ta musamman daga ofishin SGF ko kuma wata ingantacciyar majiya.
