
Daga BELLO A. BABAJI
A ranar 1 ga Afrilu ne aka samu rahoton wani mutum da ya kashe wasu mutane uku da suka yi yunƙurin bada shaida akan sa a kotu.
Lamarin ya auku ne a yankin Yovoyan – Gberefu a yankin Badagry, inda aka samu wani mai suna Charles Atideka ya buɗe wa wasu mutane uku wuta, wato Muji Onilude mai shekaru 75 da Richard Atideka mai shekaru 70 da kuma Charity Atideka mai shekaru 59.
Tuni aka garzaya da su babban Asibitin Badagry, inda aka tabbatar da mutuwarsu, kamar yadda ƴan sanda suka bayyana.
Baya ga haka ne aka kai gawarwakinsu wajen ajiyar gawa na asibitin.
A yayin haka ne aka kama wani mai suna Bright Sonu mai shekaru 33, wanda shi ya yi rakiya ga wanda ake zargin.
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Legas Benjamin Hundeyin ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ce daga nan ne aka fara neman wanda ake zargi da aikata laifin ruwa-a-jallo.
Saidai, a ranar 2 ga watan Afrilu ne aka garzaya da wanda ake zargin zuwa wani asibiti inda aka tabbatar da mutuwarsa, lamarin da ya sa ƴan sanda suka miƙa batun ga cibiyar bincike ta jihar (SCID) domin cigaba da bincike akan al’amarin.
