Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Ministan al’adu Barista Hannatu Musa Musawa ta wakilci gwamnatin tarayya,sai kwamishinan raya karkara da cigaban al’umma Farfesa Abdulhamid Ahmed Mani ya wakilci gwamnatin Jihar Katsina.
A jawabin ta bayan sun rattaɓa hannu a Katsina ministan al’adu Barista Hannatu Musawa ta cewa wannan ƙoƙari ne da shugaban ƙasa Bola Tinubu da gwamna Dikko Raɗɗa suka yi a ƙoƙarin su na farfaɗo da wuraren tarihi a Jihar Katsina.
Ta bayyana cewa bayan inganta su, za su kasance wuraren samar da kuɗaɗen shiga da Turawa da sauran al’ummar ƙasashen duniya za su rinƙa kawo ziyarar buɗe ido.
Hannatu Musawa ta ce wuraren sun haɗa da ginin Gobarau,filin Dambe na garin Katsina, rijiyar Kusugu,Durbi ta kusheyi da gidan tarihi na Katsina da sauran su.
A nasa jawabin gwamna Dikko Raɗɗa wanda kwamishinan raya karkara ya wakilta ya yabawa gwamntin tarayya da irin wannan cigaba da aka kawo wa jihar “kuma a shirye muke da yin duk abinda ya dace domin inganta rayuwar al’ummar Jihar Katsina.
Ministan ta ziyarci waɗannan wuraren tarihin da kuma kai ziyarar ban girma ga mai martaba sarkin Daura Umar Farouk Umar a fadar sa.
