Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya bayyana damuwarsa kan yadda hare-haren Boko Haram da sace-sacen mutane ke ƙara kamari a yankin, yana mai cewa hakan na nuna cewar jihar na fara rasa iko da tsaron ta. Ya bayyana haka ne a wani babban taron tsaro da aka gudanar a Maiduguri ranar Talata.
Zulum ya ce, duk da goyon bayan da gwamnatinsa ke bai wa rundunar soji da sauran hukumomin tsaro, a cikin shekaru uku da suka wuce, rahotannin kwanan nan na nuna yadda ‘yan ta’adda ke kai hari a wurare irin su Wajirko, Sabon Gari, Wulgo da Izge, tare da kashe fararen hula da jami’an tsaro, abin damuwa ne matuƙa.
Ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta ƙara tura kayan aikin zamani da na fasaha domin taimakawa wajen daƙile hare-haren da ke addabar yankunan da ke kusa da iyakar ƙasashen Chadi, Nijar da Kamaru. Ya kuma yaba da ƙoƙarin shugaba Bola Ahmed Tinubu da hukumomin tsaro bisa goyon bayan da suke bai wa jihar.
A nasa ɓangaren, Shehun Borno, Alhaji Abubakar Garbai El-Kanemi, ya ce akwai ƙananan hukumomi kamar Guzamala, Marte, Abadam da wani ɓangare na Mobbar da har yanzu Boko Haram ke riƙe da su ba tare da ikon gwamnati ba. Ya buƙaci gwamnatin tarayya da ta gaggauta gyaran manyan tituna da ke cikin jihar domin inganta tsaro da tattalin arziki.
